Tsallake zuwa abun ciki

Jezreel

22 verses

32.5500, 35.3300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jezreel

  1. Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Yezireyel, Kessulot, Shunem,

  2. Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila.

  3. Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;

  4. Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel.

  5. Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.

  6. Ana nan bayan haka sai waɗannan abubuwa suka faru. Nabot mutumin Yezireyel yana da gonar inabi a Yezireyel, a yankin Samariya, kusa da gidan Sarki Ahab.

  7. “Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’

  8. saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

  9. Game da Yezebel kuwa, karnuka za su cinye ta a fili a Yezireyel, ba kuwa wanda zai binne ta.’ ” Sa’an nan ya buɗe ƙofa ya ruga a guje.

  10. amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.”

  11. Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.

  12. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”

  13. Sa’an nan Yehu ya je Yezireyel. Sa’ad da Yezebel ta sami labari, sai ta sha kwalliya ta gyara gashin kanta, ta zauna tana kallo daga taga.

  14. Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel.

  15. Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’ ”

  16. Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.

  17. Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.

  18. Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.

  19. saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.

  20. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.

  21. Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel.

  22. ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, su kuma za su amsa wa Yezireyel.