Skip to content

Ahaziah

26 ayoyi · 5 'yan gida

An kuma san shi da: Jehoahaz, Azariah

Ayoyin da suka ambaci Ahaziah

Tace bisa littafi
  1. Yoram ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda. Sai Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  2. A shekara ta goma sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya fara mulki.

  3. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri, sarkin Isra’ila.

  4. saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

  5. Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.

  6. Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.

  7. Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”

  8. Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.

  9. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)

  10. sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.”

  11. Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.

  12. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.

  13. Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.

  14. A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.

  15. Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya, a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya tafi Urushalima ya rushe katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, ratarta ta kai wajen ƙafa ɗari shida.

  16. da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,

  17. Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da ’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa.

  18. Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.

  19. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.

  20. saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.

  21. Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.

  22. Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma ’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su.

  23. Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.

  24. Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan ’yan gidan sarautar Yahuda.

  25. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.