Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Murder

131 ayoyi · 88 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.

  2. Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini.

  3. Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.

  4. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’

  5. Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

  6. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”

  7. Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa

  8. ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku.

  9. Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta.

  10. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

  11. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.

  12. Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.

  13. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

  14. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

  15. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.

  16. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

  17. An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi

  18. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi.

  19. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne,

  20. “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;

  21. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

  22. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  23. waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane

  24. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,

  25. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.