Skip to content

Shechem

40 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Sichem

32.2100, 35.2800 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Shechem

Tace bisa littafi
  1. Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar.

  2. Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.

  3. Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.

  4. Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem.

  5. To, ’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem.

  6. Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani, ’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.” Ya ce, “To.”

  7. Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem,

  8. Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa.

  9. Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.

  10. A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer,

  11. Yoshuwa ya tattara dukan kabilan Isra’ila a Shekem. Ya aika a kira dattawa, shugabanni, alƙalai da manyan ma’aikatan Isra’ila, suka kai kansu gaban Allah.

  12. A wannan rana Yoshuwa ya yi alkawari saboda mutanen, kuma a can Shekem ya tsara musu ƙa’idodi da dokoki.

  13. Aka kuma binne ƙasusuwan Yusuf da aka kawo daga Masar, a Shekem a wurin da Yaƙub ya saya da azurfa ɗari daga ’ya’yan Hamor, babban Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusuf.

  14. Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek.

  15. Abimelek ɗan Yerub-Ba’al ya tafi Shekem wurin ’yan’uwan mahaifiyarsa, ya ce musu da kuma dukan dangin mahaifiyarsa,

  16. “Ku tambayi ’yan ƙasar Shekem, ‘Wanne ya fi muku, a sa dukan ’ya’yan Yerub-Ba’al saba’in maza su yi mulkinku, ko dai mutum guda kawai yă yi mulkinku?’ Ku tuna, ni jininku ne.”

  17. Sa’ad da ’yan’uwan suka mayar wa ’yan ƙasar Shekem wannan, sai suka goyi bayan Abimelek, gama sun ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.”

  18. Sa’an nan duka ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo suka taru kusa da babban itacen wajen ginshiƙi a Shekem don a naɗa Abimelek sarki.

  19. Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni, ’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku.

  20. (amma ga shi yau kun tayar wa iyalin mahaifina, kuka kashe ’ya’yansa saba’in a dutse guda, kuka kuma naɗa Abimelek, ɗan baiwa, sarki a kan ’yan ƙasar Shekem domin shi ɗan’uwanku ne)

  21. Amma in ba haka ba, bari wuta ta fito daga Abimelek ya cinye ku, ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo, bari wuta kuma daga wurinku ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek!”

  22. sai Allah ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka ci amanar Abimelek.

  23. Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa.

  24. Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.

  25. To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi.