Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Benjamin

107 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.

  2. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  3. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  4. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  5. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  6. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.

  7. Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu, daga Bela, kabilar Belawa; daga Ashbel, kabilar Ashbelawa; daga Ahiram, kabilar Ahiramawa;

  8. daga Shufam, kabilar Shufamawa; daga Hufam, kabilar Hufamawa.

  9. Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman, daga Ard, kabilar Ardawa; daga Na’aman, kabilar Na’amawa;

  10. Ƙuri’ar kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. Rabonsu ya kama daga ƙasar da take tsakanin kabilar Yahuda da ta Yusuf.

  11. Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen.

  12. Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon.

  13. Daga tudun da yake fuskantar Bet-Horon a kudu, iyakar ta juya kudu ta gefen yamma ta ɓullo a Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim), birnin Yahuda. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

  14. A gefen kudu kuwa, iyakar ta fara daga ƙauyukan Kiriyat Yeyarim wajen yamma sai ta miƙe zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa.

  15. Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel.

  16. Sai ta nausa ta yi wajen arewa, zuwa En Shemesh, ta ci gaba zuwa Gelilot, wanda yake fuskantar hawan Adummim. Daga can ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ruben.

  17. Sai ta wuce ta yi arewancin gangaren Bet-Araba, ta wuce har zuwa cikin Araba.

  18. Sa’an nan ta wuce zuwa arewancin gangaren Bet-Hogla ta kuma ɓulla a arewancin gaɓar Tekun Gishiri, a bakin Urdun a kudu. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

  19. Urdun shi ne iyaka a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Benyamin suka gāda.

  20. Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo. Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz,

  21. Bet-Araba, Zemarayim, Betel,

  22. Awwim, Fara, Ofra,

  23. Kefar Ammoni, Ofni da Geba, garuruwa goma sha biyu ke nan da ƙauyukansu.

  24. Akwai kuma Gibeyon, Rama, Beyerot,

  25. Mizfa Kefira, Moza,