Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Benjamin

107 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Rekem, Irfeyel, Tarala,

  2. Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon kabilar Benyamin bisa ga iyalansu.

  3. Kabilan Isra’ila suka aika jakadu a ko’ina a cikin kabilar Benyamin cewa, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?

  4. Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!” Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba.

  5. Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa.

  6. Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya.

  7. Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure.

  8. Isra’ila kuwa, ban da Benyamin, sun tara mayaƙa masu takobi dubu ɗari huɗu, dukansu gwanayen yaƙi ne.

  9. Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?” Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”

  10. Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya.

  11. Mutanen Isra’ila suka fita yaƙi da mutane Benyamin suka kuma ja dāgār yaƙi a Gibeya.

  12. Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar.

  13. Amma mutanen Isra’ila suka ƙarfafa juna, suka sāke koma inda suka ja dāgā a rana ta farko.

  14. Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?” Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.”

  15. Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu.

  16. A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.

  17. Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.

  18. Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can,

  19. Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?” Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.”

  20. Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya.

  21. Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā.

  22. Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya.

  23. Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.”

  24. Dukan mutanen Isra’ila suka taso daga wurarensu suka ja dāgā a Ba’al-Tamar, Isra’ilawan da suka yi kwanto a yammancin Geba kuwa suka fito.

  25. Sa’an nan jarumai Isra’ila dubu goma suka yi gaba suka kai wa Gibeya hari. Yaƙi kuwa ya yi zafi har mutane Benyamin ba su san masifa tana dab da su ba.