Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribe Of Benjamin: Some of, assisted David
Ayoyi game da Some of, assisted David
Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi;
suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot,
da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera,
Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.