Tsallake zuwa abun ciki

Bethel

62 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Beth-el, house

31.9300, 35.2200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Bethel

Tace bisa littafi
  1. Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.

  2. Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari

  3. Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.

  4. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ”

  5. Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”

  6. Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.”

  7. Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana.

  8. To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.

  9. Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.

  10. Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.

  11. Sai Yoshuwa ya aika mutane daga Yeriko zuwa Ai kusa da Bet-Awen gabas da Betel, ya ce musu, “Ku je ku leƙo ku ga yadda yankin yake.” Sai mutanen suka je suka leƙo asirin ƙasar Ai.

  12. Sai Yoshuwa ya sallame su, suka kuma tafi wurin da za su yi kwanto, suka kwanta suna fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma Yoshuwa ya kwana tare da mutanen.

  13. Yoshuwa ya sa mutum dubu biyar suka yi kwanto tsakanin Betel da Ai, a yammancin birnin.

  14. Ba namijin da ya rage a Ai ko Betel da bai fita don yă fafari Isra’ilawa ba. Suka bar birnin a buɗe, suka tafi fafarar Isra’ilawa.

  15. Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya

  16. Rabon da aka ba wa Yusuf ya fara tun daga Urdun kusa da Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, sai ya miƙe zuwa jeji, ya haura har zuwa cikin ƙasar tudu na Betel.

  17. Ya ci gaba daga Betel (wato, Luz), ya zarce zuwa sashen Arkitawa na Atarot,

  18. Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon.

  19. Bet-Araba, Zemarayim, Betel,

  20. To, gidan Yusuf suka auka wa Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.

  21. Sa’ad da suka aike mutane don su leƙi asirin Betel (da dā ake kira Luz),

  22. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.

  23. Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?” Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”

  24. Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.

  25. Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya.