Tsallake zuwa abun ciki

Babylon

255 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Babylon's, Sheshach

32.5300, 44.4200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Babylon

Tace bisa littafi
  1. za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!

  2. “Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.

  3. Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’ ”

  4. A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa.

  5. Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”

  6. Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji.

  7. Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”

  8. Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.

  9. “Ki gangara, ki zauna a ƙura, Budurwa Diyar Babilon; ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba, Diyar Babiloniyawa. Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba.

  10. “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.

  11. Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”

  12. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.

  13. Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon.

  14. Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”

  15. “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.”

  16. ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.

  17. Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’

  18. Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’

  19. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.

  20. Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji.

  21. Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon.

  22. zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada.

  23. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.

  24. “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada.

  25. da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.