Skip to content

Sea

12 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Great Sea

33.2400, 33.4700 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Sea

  1. “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.

  2. “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,

  3. Ƙasar da ta kama daga hamada zuwa Lebanon, zuwa babban Kogin, wato, Kogin Yuferites, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum, wajen yamma.

  4. To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa)

  5. Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu.

  6. Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.

  7. Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma.

  8. Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum.

  9. “Wannan ce za tă zama iyakar ƙasa. “A wajen arewa za tă fara daga Bahar Rum ta hanyar Hetlon ta wuce Lebo Hamat zuwa Zedad,

  10. A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

  11. A wajen yamma, Bahar Rum ne zai zama iyakar zuwa wani wuri ɗaura da Lebo Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

  12. Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum.