Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Hittites

13 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka

  2. ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.

  3. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.

  4. Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.

  5. To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa)

  6. suka haɗa kansu don su yaƙi Yoshuwa da Isra’ila.

  7. Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa.

  8. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.

  9. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.

  10. Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne),

  11. wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau.

  12. Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne),

  13. wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.