Tsallake zuwa abun ciki

Canaan

89 ayoyi · 15 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Canaan

Tace bisa littafi
  1. ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)

  2. Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje.

  3. sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.”

  4. Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.

  5. Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”

  6. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.

  7. Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,

  8. Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.

  9. Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.

  10. Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom.

  11. Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.

  12. Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu.”

  13. Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.

  14. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.

  15. Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.

  16. Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,”

  17. Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba;

  18. ya kuma kora dukan dabbobinsa, suka ja gabansa, tare da dukan abubuwan da ya samu a Faddan Aram, don su tafi wurin mahaifinsa Ishaku a ƙasar Kan’ana.

  19. Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.

  20. Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana.

  21. Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye

  22. Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.

  23. Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.

  24. Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.

  25. Sai ’ya’yan Yaƙub suka isa Masar tare da sauran mutanen don sayen abinci, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana ma.