Skip to content

Ham

14 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ham

  1. Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.

  2. Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.

  3. A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.

  4. ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)

  5. Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje.

  6. Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.

  7. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.

  8. Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

  9. ’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet.

  10. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.

  11. Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.

  12. Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.

  13. Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.

  14. mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.