Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Anger of God

46 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane.

  2. Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu.

  3. Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.

  4. Kashegari da sassafe suka haura ta wajen ƙasa mai tudu suka ce, “Mun yi zunubi, za mu tafi inda Ubangiji ya yi alkawari.”

  5. Amma Musa ya ce, “Don me kuke rashin biyayya da umarnin Ubangiji? Wannan ba zai yiwu ba!

  6. Kada ku haura, domin Ubangiji, ba ya tare da ku. Magabtanku za su ci nasara a kanku,

  7. gama Amalekawa da Kan’aniyawa za su kara da ku a can. Domin kun juya daga Ubangiji, ba zai kasance da ku ba, za a kuma karkashe ku da takobi.”

  8. Duk da haka, suka yi tsammani ba zai zama haka ba, sai suka haura ta wajen ƙasa mai tudu, Musa da akwatin alkawarin Ubangiji dai ba su gusa daga sansanin ba.

  9. Sai Amalekawa da Kan’aniyawa mazaunan ƙasar tudu, suka gangaro suka auka musu, suka bubbuge su suka kokkore su har Horma.

  10. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.

  11. Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?

  12. Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

  13. Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.

  14. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.

  15. Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.

  16. “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,

  17. in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,

  18. zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala;

  19. An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka.

  20. Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.

  21. Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi.

  22. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  23. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  24. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  25. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.