- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Anger of God
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’
Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji.
“Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?
“Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi.
“Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.”
“Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”
Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.
Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku.
Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can.
Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu,
rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi.
“Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.
Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.
Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.
Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’
Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.
Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.