Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shem

81 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.

  2. Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.

  3. A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi.

  4. ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)

  5. Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.

  6. Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi,

  7. sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.”

  8. Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.

  9. Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”

  10. Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.

  11. Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.

  12. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

  13. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.

  14. Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

  15. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.

  16. Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,

  17. Hadoram, Uzal, Dikla,

  18. Obal, Abimayel, Sheba,

  19. Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

  20. Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.

  21. Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

  22. Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.

  23. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  24. Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.

  25. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.