Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shem: Descendants of

70 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Descendants of

Tace bisa littafi
  1. Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.

  2. Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.

  3. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

  4. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.

  5. Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

  6. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.

  7. Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,

  8. Hadoram, Uzal, Dikla,

  9. Obal, Abimayel, Sheba,

  10. Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

  11. Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.

  12. Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

  13. Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.

  14. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  15. Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.

  16. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  17. Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.

  18. Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  19. Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.

  20. Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  21. Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.

  22. Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  23. Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.

  24. Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  25. Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.