Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Phut

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.

  2. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.

  3. Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka.

  4. “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.

  5. Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.

  6. Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano,

  7. Kush da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka; Fut da Libiya suna cikin mataimakanta.