Skip to content

Lud

4 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Lydia, Lydians

31.9500, 34.8900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Lud

  1. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.

  2. Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka.

  3. “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.

  4. Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.