- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Asher
An kuma san shi da: Aser
Ayoyin da suka ambaci Asher
Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.
’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya. ’Yar’uwarsu ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel.
“Abincin Asher zai zama a wadace, zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
Dan da Naftali; Gad da Asher.
daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;
Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne.
Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran.
A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.
Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher,
Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;
Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa;
(Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.)
Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.
Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.
Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai.
Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa.
Ƙasar a wajen kudu ta Efraim ce, ta wajen arewa kuma ta Manasse ce. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Asher yana wajen arewa, Issakar kuma a wajen gabas.
A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot).
Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.
Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
Aka kuma ba wa zuriyar Gershon garuruwa goma sha uku daga iyalan kabilan Issakar, Asher, Naftali, da kuma rabin kabilar Manasse a Bashan.