Tsallake zuwa abun ciki

Ebal

5 verses

32.2300, 35.2700 Duba a Google Maps

Nemi "Ebal"

Ayoyin da suka ambaci Ebal

  1. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.

  2. Sa’ad da kuma kuka haye Urdun, ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal, kamar yadda na umarce a yau, ku yi musu shafe da farar ƙasa.

  3. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

  4. Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,

  5. Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.