Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Asher

29 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.

  2. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  3. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  4. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  5. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  6. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.

  7. Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa;

  8. daga zuriyar Beriya kuwa, daga Heber, kabilar Heberawa; daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa.

  9. (Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.)

  10. Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.

  11. Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.

  12. Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf,

  13. Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.

  14. Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,

  15. ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.

  16. Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,

  17. Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.

  18. Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.

  19. ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya. ’Yar’uwarsa ita ce Sera.

  20. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit.

  21. Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa.

  22. ’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaflet maza.

  23. ’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram.

  24. ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal.

  25. ’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra,