Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Holy Land

108 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.

  2. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”

  3. Ubangiji ya ce wa Musa,

  4. “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.

  5. Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.

  6. “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

  7. Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon

  8. Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;

  9. Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;

  10. Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;

  11. Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;

  12. Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;

  13. Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;

  14. Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;

  15. Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”

  16. Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.

  17. Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;

  18. ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma;

  19. ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

  20. Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.

  21. Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.

  22. Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

  23. In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam,

  24. Ubangiji zai kori dukan waɗannan al’ummai a gabanku, za ku kuma kore al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.

  25. Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.