Tsallake zuwa abun ciki

Joshua

189 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Oshea, Jehoshua, Hoshea, Jeshua, Jesus

Ayoyin da suka ambaci Joshua

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.”

  2. Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane.

  3. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  4. Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,

  5. Saboda haka sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane,

  6. Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse,

  7. Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Duk abin da ka ce mu yi, za mu yi. Duk inda kuma ka aike mu, za mu je.

  8. Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can.

  9. Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.

  10. Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”

  11. Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.

  12. Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.”

  13. Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku sha gaba.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban sauran jama’a.

  14. Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa.

  15. Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.

  16. Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.

  17. Da al’umma gaba ɗaya suka ƙetare Urdun, Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,

  18. Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila

  19. ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,

  20. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.

  21. Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.

  22. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.

  23. A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa.

  24. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,

  25. Sai Yoshuwa ya umarci firistoci ya ce, “Ku fito daga cikin Urdun.”