Tsallake zuwa abun ciki

Creation Era

The Tower of Babel

Scattered nations and confused languages mark the beginning of the diversity of peoples across the earth.

64 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 10:26kusan 2247 K.H.

    Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,

  2. Farawa 10:27kusan 2247 K.H.

    Hadoram, Uzal, Dikla,

  3. Farawa 10:28kusan 2207 K.H.

    Obal, Abimayel, Sheba,

  4. Farawa 10:29kusan 2207 K.H.

    Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

  5. Farawa 10:30kusan 2207 K.H.

    Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.

  6. Farawa 10:31kusan 2207 K.H.

    Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

  7. Farawa 10:32kusan 2207 K.H.

    Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.

  8. Farawa 11:1kusan 2247 K.H.

    To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.

  9. Farawa 11:2kusan 2247 K.H.

    Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

  10. Farawa 11:3kusan 2247 K.H.

    Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.

  11. Farawa 11:4kusan 2247 K.H.

    Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  12. Farawa 11:5kusan 2247 K.H.

    Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.

  13. Farawa 11:6kusan 2247 K.H.

    Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.

  14. Farawa 11:7kusan 2247 K.H.

    Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”

  15. Farawa 11:8kusan 2247 K.H.

    Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.

  16. Farawa 11:9kusan 2247 K.H.

    Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

  17. Farawa 11:10kusan 2346 K.H.

    Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.

  18. Farawa 11:11kusan 1846 K.H.

    Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  19. Farawa 11:12kusan 2311 K.H.

    Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.

  20. Farawa 11:13kusan 1908 K.H.

    Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  21. Farawa 11:14kusan 2281 K.H.

    Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.

  22. Farawa 11:15kusan 1878 K.H.

    Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  23. Farawa 11:16kusan 2247 K.H.

    Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.

  24. Farawa 11:17kusan 1817 K.H.

    Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

  25. Farawa 11:18kusan 2217 K.H.

    Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.