Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tongue

56 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)

  2. Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

  3. To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.

  4. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

  5. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.

  6. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  7. Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.

  8. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.

  9. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”

  10. Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.

  11. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

  12. Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.

  13. Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

  14. Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.

  15. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.

  16. Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.

  17. Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.

  18. “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.

  19. Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.

  20. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.

  21. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.

  22. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

  23. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.

  24. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.

  25. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?