Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tongue

56 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?

  2. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,

  3. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma

  4. (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”

  5. A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”

  6. Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”

  7. Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.

  8. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!

  9. A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

  10. “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.

  11. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.

  12. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.

  13. Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah. Sai Bitrus ya ce,

  14. Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci.

  15. Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.

  16. A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.

  17. Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara?

  18. In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.

  19. Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani.

  20. Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

  21. Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya.

  22. Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.

  23. Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana.

  24. Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

  25. Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa,