Skip to content

Mesopotamia

7 verses

32.5300, 44.4200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Mesopotamia

  1. Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.

  2. Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku.

  3. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas.

  4. Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa.

  5. Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.

  6. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,

  7. Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.