Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Medo-Persian Kingdom

62 ayoyi · 34 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe.

  2. A kuma koya mata yadda za tă tafi wurin sarki. Aka ba ta duk abin da take so ta riƙe daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki.

  3. Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.

  4. Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.”

  5. “Dukan hafsoshin sarki da mutanen lardunan sarki sun san cewa duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, mace ko namiji, ba tare da an kira shi ba, doka ɗaya ce take kan mutum, wato, kisa. Abu guda kawai da ya sha bamban shi ne sai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don yă rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”

  6. “Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.”

  7. Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.

  8. Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!”

  9. ’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha.

  10. Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha.

  11. Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku. Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu, mai hari ya zo daga hamada, daga ƙasar mai banrazana.

  12. An nuna mini mugun wahayi, mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe. Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto! Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.

  13. wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’

  14. “Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.

  15. Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.

  16. Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.

  17. Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.

  18. “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.

  19. Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano,

  20. An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne.

  21. “A bayanka, za a yi wani mulki, wanda bai kai naka ba. A gaba kuma, za a yi mulki na uku wanda yake na tagulla, zai yi mulkin dukan duniya.

  22. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

  23. “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.”

  24. Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.

  25. Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar,