Skip to content

Artaxerxes

10 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Artaxerxes

  1. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.

  2. Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya,

  3. Waɗansu Isra’ilawa, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali su ma suka zo Urushalima a shekara ta bakwai a zamanin mulkin sarki Artazerzes.

  4. Ga wasiƙar da sarki Artazerzes ya ba Ezra wanda yake firist da kuma malami, mutumin da yake cike da sani game da dokoki da kuma umarnan Ubangiji wa Isra’ila.

  5. Artazerzes, sarkin sarakuna. Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama. Gaisuwa.

  6. Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci,

  7. Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.

  8. A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo.

  9. Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.

  10. Amma yayinda dukan wannan yake faruwa, ba ni a Urushalima, gama a shekara ta talatin da biyu na Artazerzes sarkin Babilon na dawo wurin sarki. A wani lokaci daga baya na nemi izininsa