Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Months

42 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,

  2. A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.

  3. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.

  4. Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,

  5. A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib.

  6. Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

  7. Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”

  8. Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.

  9. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.

  10. A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.

  11. An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif.

  12. A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.

  13. Dukan mutanen Isra’ila suka tattaru a gaban Sarki Solomon a lokacin biki, a watan Etanim, wato, wata na bakwai.

  14. Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  15. Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.

  16. Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  17. Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.

  18. Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.

  19. Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  20. Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  21. Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  22. Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  23. Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  24. Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  25. Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.