Skip to content

Anathoth

15 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Anetothite

31.8100, 35.2600 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Anathoth

  1. Anatot da Almon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

  2. Ga Abiyatar firist kuwa sarki ya ce, “Tafi gonarka a Anatot. Ka cancanci ka mutu, amma ba zan kashe ka yanzu ba, domin ka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji Mai Iko Duka a gaban mahaifina Dawuda, ka kuma sha wahala tare mahaifina.”

  3. Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.

  4. Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  5. na Anatot 128

  6. na Anatot 128

  7. da Anatot, da Nob, da Ananiya,

  8. Ki yi ihu, ya Diyar Gallim! Ki saurara, ya Layisha! Kayya, Anatot abin tausayi!

  9. Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin.

  10. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’

  11. Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ”

  12. To, me ya sa ba ka tsawata wa Irmiya daga Anatot, wanda yana ɗauka kansa annabi a cikinku ba?

  13. Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’

  14. “Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce;

  15. saboda haka sai na saye filin a Anatot daga hannun Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina na kuma auna masa shekel goma sha bakwai na azurfa.