Skip to content

Darius

16 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Darius

  1. Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa.

  2. Saboda haka aikin a gidan Allah a Urushalima ya tsaya cik sai a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus sarkin Farisa.

  3. Amma Allah yana tsaron dattawan Yahudawa, saboda haka ba a hana su aikin ba har sai rahoto ya kai wurin Dariyus aka kuma sami amsarsa a rubuce tukuna.

  4. Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus.

  5. Ga rahoton da suka aika masa. Zuwa ga Sarki Dariyus. Gaisuwa da fatan alheri.

  6. Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.

  7. Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima. Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa.

  8. Saboda umarnin da sarki Dariyus ya aika, sai Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites da Shetar-Bozenai da abokansu suka yi biyayya da umarnin babu wasa.

  9. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.

  10. An gama ginin haikalin a rana ta uku na watan Adar a shekara ta shida ta mulkin Sarki Dariyus.

  11. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.

  12. a ranar ashirin da huɗu ga watan shida. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus,

  13. A ranar ashirin da huɗu ga watan tara, a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai cewa,

  14. A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

  15. 7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

  16. A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.