Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Love of Country

55 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya. A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha.

  2. Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.

  3. Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”

  4. Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama.

  5. Na ce, “Ya Ubangiji Allah na sama, Allah mai girma da mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna da waɗanda suke ƙaunarsa, suke kuma yin biyayya da umarnansa,

  6. ka sa kunne ka kuma buɗe idanunka ka ji addu’ar da bawanka yake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Na furta zunuban da mu Isra’ilawa, har da ni da kuma gidan mahaifina muka yi maka.

  7. Mun yi mugunta gare ka. Ba mu yi biyayya da umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da ka ba wa bawanka Musa ba.

  8. “Ka tuna da umarnan da ka ba wa bawanka Musa, kana cewa, ‘In kun yi rashin aminci, zan warwatsar da ku a cikin al’ummai,

  9. amma in kuka dawo gare ni kuka kuma yi biyayya da umarnaina, to, ko mutanenku da aka kwasa zuwa zaman bauta suna can wuri mafi nisa, zan tattara su daga can in kawo su wurin da na zaɓa yă zama wurin zama don Sunana.’

  10. “Su bayinka ne da kuma mutanenka da ka fansa ta wurin ƙarfinka mai girma da kuma hannunka mai iko.

  11. Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar wannan bawanka da kuma ga addu’ar bayinka waɗanda suke farin cikin girmama sunanka. Ka ba wa bawanka nasara a yau ta wurinsa yă sami tagomashi a gaban wannan mutum.” Ni ne mai riƙon kwaf sarki.

  12. A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo.

  13. Saboda haka sarki ya tambaye ni ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake ba? Ba abin da ya kawo wannan, in ba dai kana baƙin ciki ba.” Sai na ji tsoro ƙwarai,

  14. na amsa na ce wa sarki, “Ran sarki yă daɗe! Me zai hana fuskata ta ɓaci, sa’ad da birnin da aka binne kakannina tana zaman kango, aka kuma rushe ƙofofinsa da wuta?”

  15. Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama,

  16. na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, “In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi.”

  17. Sai sarki, a lokacin sarauniya da tana zama kusa da shi, ya tambaye ni, ya ce, “Kwana nawa tafiyar za tă ɗauke ka, kuma yaushe za ka dawo?” Ya gamshi sarki ya aike ni; saboda haka na shirya lokaci.

  18. Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda?

  19. A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.

  20. Saboda haka na tafi wurin gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, na ba su wasiƙun sarki. Sarki kuma ya aika da hafsoshin mayaƙa da kuma mahayan dawakai tare da ni.

  21. Da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon suka ji cewa wani ya zo domin yă ƙarfafa zaman lafiyar mutanen Isra’ila, sai suka damu ƙwarai.

  22. Sai na je Urushalima, bayan na zauna a can na kwanaki uku,

  23. sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

  24. Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.

  25. Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;