Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Love of Country

55 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari.

  2. Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da nake yi ba, domin ban riga na faɗa wa Yahudawa, ko firistoci, ko manyan gari, ko shugabanni, ko sauran waɗanda za su yi aiki, kome ba.

  3. Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.”

  4. Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau.

  5. Amma sa’ad da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon da kuma Geshem mutumin Arab suka ji game da wannan, sai suka yi mana ba’a suka kuma yi mana dariya. Suka ce, “Me kuke tsammani kuke yi? Kuna so ku yi wa sarki tawaye ne?”

  6. Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.”

  7. To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan ’yan’uwansu Yahudawa.

  8. Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.”

  9. Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

  10. Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.

  11. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”

  12. Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai.

  13. Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa ’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan.

  14. Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi ’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da ’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!”

  15. Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba?

  16. Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa!

  17. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

  18. Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.

  19. Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.

  20. Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.

  21. Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.

  22. A maimakon haka, na miƙa kaina ga aiki a kan wannan katanga. Na tattara dukan mutanena a can don aikin; ba mu samar wa kanmu wata gona ba.

  23. Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye.

  24. Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa.

  25. A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.