Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zerubbabel

28 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.

  2. Ga lissafin kayan. Manyan kwanonin zinariya guda 30 Manyan kwanonin azurfa guda 1,000 Wuƙaƙe guda 29

  3. Waɗansu kwanonin zinariya guda 30 Waɗansu kwanonin azurfa guda 410 da waɗansu kayayyaki guda 1,000

  4. Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima.

  5. Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah.

  6. Duk da tsoron da suke ji na mutanen da suke kewaye da su, sun gina bagaden a wurinsa, suka kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagaden ga Ubangiji safe da yamma.

  7. Bisa ga abin da yake a rubuce kuma, suka yi biki Bikin Tabanakul, suka miƙa hadayu kowace rana gwargwadon yawan hadayun da ake bukata.

  8. Bayan wannan, suka miƙa hadayu na ƙonawa yadda aka saba. Suka miƙa hadayu na Sabon Wata, da hadayu na bukukkuwan Ubangiji, da kuma hadayun da aka bayar da yardar rai ga Ubangiji.

  9. A ranar farko ta watan bakwai, sai suka fara miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko da yake ba a riga an aza harsashin ginin haikalin Ubangiji ba.

  10. Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.

  11. A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.

  12. sai suka zo wurin Zerubbabel da kuma wurin shugabannin iyalai, suka ce, “Bari mu taimake ku ginin domin mu ma muna addu’a ga Allahnku yadda kuke yi, muna miƙa masa hadaya tun lokacin Esar-Haddon sarkin Assuriya wanda ya kawo mu nan.”

  13. Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.”

  14. Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu.

  15. Ya kuma kwashe kwanonin zinariya da azurfa na gidan Allah daga haikalin Babilon waɗanda Nebukadnezzar ya kwasa daga haikali a Urushalima. Sa’an nan sarki Sairus ya ba wa wani mutum mai suna Sheshbazzar umarni wanda ya sa ya zama gwamna,

  16. ya ce masa, ‘Ka kwashe kayan nan ka je ka zuba su a cikin haikalin Allah a Urushalima. Ka kuma sāke gina gidan Allah a wurin da yake a dā.’

  17. “Saboda haka Sheshbazzar ya so ya aza harsashin gina gidan Allah a Urushalima. Tun daga wancan lokaci har zuwa yau ana kan gina shi amma ba a gama ba.”

  18. Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji.

  19. Sai Haggai, ɗan saƙon Ubangiji, ya ba da wannan saƙo na Ubangiji ga mutane cewa, “Ina tare da ku” in ji Ubangiji.

  20. Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu,

  21. “Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce,

  22. Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  23. “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”

  24. Sai maganar Ubangiji ta zo mini,

  25. “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka.