Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sea

95 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.

  2. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  3. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.

  4. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  5. Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.

  6. “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.

  7. Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),

  8. “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.

  9. An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,

  10. Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.

  11. A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa.

  12. Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.

  13. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.

  14. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.

  15. Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  16. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

  17. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.

  18. Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su

  19. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata.

  20. Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku.