Skip to content

Andrew

12 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Andrew

  1. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  2. Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;

  3. Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne.

  4. Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.

  5. Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  6. Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,

  7. Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,

  8. Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.

  9. Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.

  10. Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,

  11. Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.

  12. Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.