Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thomas

15 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

  2. Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  3. Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  4. Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”

  5. Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”

  6. Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo.

  7. Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!” Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.”

  8. Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

  9. Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”

  10. Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”

  11. Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”

  12. Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.

  13. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.

  14. Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.

  15. Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.