Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thomas: Sees Jesus after the resurrection

6 ayoyi · 8 fannoni

Ayoyi game da Sees Jesus after the resurrection

  1. Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

  2. Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”

  3. Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”

  4. Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”

  5. Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.

  6. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.