Skip to content

Matthew

8 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Levi

Ayoyin da suka ambaci Matthew

  1. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

  2. Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

  3. Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.

  4. Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  5. Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”

  6. Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.

  7. Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  8. Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.