Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Apostles

90 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  2. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

  3. Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

  4. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,

  5. nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

  6. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  7. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  8. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  9. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

  10. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.

  11. Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;

  12. Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

  13. Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

  14. Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?

  15. Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike?

  16. Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

  17. Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

  18. Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

  19. Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.

  20. Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba.

  21. Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”

  22. Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

  23. Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”

  24. Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.

  25. Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”