Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Apostles: Fail to comprehend the nature and mission of Jesus, and the nature of the kingdom He came to establish

36 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Fail to comprehend the nature and mission of Jesus, and the nature of the kingdom He came to establish

Tace bisa littafi
  1. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  2. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  3. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  4. Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?

  5. Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike?

  6. Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

  7. Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

  8. Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

  9. Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

  10. Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”

  11. Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,

  12. gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.

  13. Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?

  14. Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?

  15. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

  16. Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”

  17. gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”

  18. Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.

  19. Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.

  20. Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.

  21. “Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.”

  22. Amma ba su fahimci abin da yake nufi da wannan magana ba. Ba su gane ba, don an ɓoye musu shi. Su kuwa sun ji tsoro su tambaye shi.

  23. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”

  24. Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”

  25. Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.”