Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Apostles: Selection of

21 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Selection of

  1. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  2. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

  3. Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

  4. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,

  5. nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

  6. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

  7. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.

  8. Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;

  9. Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

  10. Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

  11. Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.

  12. Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi,

  13. don kuma su sami ikon fitar da aljanu.

  14. Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);

  15. Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);

  16. Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  17. da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

  18. Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.

  19. Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,

  20. Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,

  21. Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.