Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sea

95 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.

  2. Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

  3. Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.

  4. A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa.

  5. gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.

  6. wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.

  7. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,

  8. Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,

  9. Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.

  10. Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.

  11. Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su.

  12. Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.

  13. Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.

  14. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

  15. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.

  16. A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

  17. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

  18. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.

  19. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.

  20. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.

  21. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.

  22. Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.

  23. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

  24. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,

  25. sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.