Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus: Death of

54 ayoyi · 25 fannoni

Ayoyi game da Death of

Tace bisa littafi
  1. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba.

  2. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.

  3. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa.

  4. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.

  5. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu.

  6. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.

  7. A ranan nan zan fito don in hallaka dukan al’umman da suka yaƙi Urushalima.

  8. “Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.

  9. In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’

  10. “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.

  11. Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”

  12. Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.

  13. Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.

  14. Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.

  15. To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu,

  16. “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa

  17. za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

  18. “Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.

  19. Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.

  20. “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.

  21. Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.

  22. A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’

  23. “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’

  24. Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.

  25. Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.