Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus: Receives the rich young ruler, who asks what he shall do to inherit eternal life (Peraea)

20 ayoyi · 25 fannoni

Ayoyi game da Receives the rich young ruler, who asks what he shall do to inherit eternal life (Peraea)

  1. Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.

  2. Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.

  3. Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,

  4. gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.

  5. “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.

  6. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.

  7. To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

  8. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

  9. Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,

  10. ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”

  11. Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

  12. Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

  13. Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

  14. Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.

  16. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

  17. Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”

  18. Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”

  19. Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai.

  20. Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!