Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus: Obedience of Jesus
Ayoyi game da Obedience of Jesus
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba.
Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.
Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”
Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).
Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun.