Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus: Holiness of

7 ayoyi · 25 fannoni

Ayoyi game da Holiness of

  1. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.

  2. Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.

  3. Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?

  4. Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

  5. Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama.

  6. Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa.

  7. Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.