Skip to content

Satan

55 ayoyi

An kuma san shi da: Beelzebub

Ayoyin da suka ambaci Satan

Tace bisa littafi
  1. Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila.

  2. Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.

  3. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”

  4. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”

  5. Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah?

  6. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.

  7. Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa.

  8. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”

  9. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”

  10. Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa.

  11. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”

  12. Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa.

  13. Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.

  14. Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi.

  15. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”

  16. Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”

  17. Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub,me za su ce game da mutanen gidansa?

  18. Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”

  19. In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?

  20. In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

  21. Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”

  22. ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.

  23. Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

  24. Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?

  25. In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.